Westwood ya sabunta kwantiragi da Aston Villa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Westwood na fatan ya kammala wasanninsa a Villa

Dan kwallon Aston Villa mai buga mata wasan tsakiya Ashley Westwood ya tsawaita zamansa a kulob din zuwa shekaru biyar.

Westwood mai shekaru 25, ya koma Villa daga kungiyar One Crewe mai buga gasar League One kan kudi £2m a 2012.

Dan wasan dan kasar Ingila ya buga wa Villa wasanni 103, ciki har da karawa 29 a bara, bayan da kungiyar ta kai wasan karshe a kofin FA.

Westwood ya fada a shafin intanet na kulob din cewar yanzu ya kai ganiyarsa a harkar tamaula, kuma yana fatan ya kammala wasanninsa a Aston Villa.