U-17: "Nigeria za ta taka rawa a Chile"

Image caption Nigeria ce ke rike da kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 ta duniya

Kocin tawagar kwallon kafar matasa na Nigeria 'yan kasa da shekaru 17 Emmanuel Amuneke ya ce tawagar za ta kara kaimi kafin ta fara karawa a gasar kofin matasa ta duniya da za a yi a Chile.

Tawagar Nigeria tana rukuni na daya da ya kunshi Chile da Croatia da kuma Amurka.

Nigeria wacce ke rike da kofin ta samu kaiwa gasar ne da kyar, bayan da ta yi ta hudu a wasannin neman gurbin nahiyar Afirka da aka yi a watan Maris.

Amuneke ya ce suna cikin rukuni mai tsauri da ya kunshi mai masaukin baki da kuma kasashe biyu manya a fagen tamaula.

Kocin ya kara da cewa shirin da yake yi shi ne ya lashe wasan farko da Amurka, domin nasara a karawar farko za ta ba su damar tunkarar sauran wasannin cikin natsuwa.

Kuma ya ce zai mai da hankali wajen da suke da matsala tun daga mai tsaron raga har zuwa wajen masu zura kwallo a raga.

Ga jadawalin wasannin matasan 'yan kasa da shekaru 17:

  • Rukunin A: Chile, Croatia, Nigeria, USA
  • Rukunin D: Belgium, Mali, Honduras, Ecuador
  • Rukunin B: England, Guinea, Brazil, South Korea
  • Rukunin: South Africa, Costa Rica, North Korea, Russia
  • Rukunin C: Australia, Germany, Mexico, Argentina
  • Rukunin F: New Zealand, France, Syria, Paraguay