Zaben gwarzon 'yan kwallon Turai

Image caption Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Turai a bara

Hukumar kwallon kafar Turai ta fitar da sunayen 'yan wasan kwallon kafa su 10, wadan da za a zabi gwarzon dan wasan da yafi yin fice a nahiyar ranar 27 ga watan Agusta.

Kamar yadda dai aka yi a bara, fitattun 'yan jaridu da ke cikin mambobin kasashe 54 na Uefa ne suka zakulo 'yan wasan 10, kafin a kuma fitar da ukun farko ranar 12 ga Agusta.

A kuma ranar 27 ga watan Agusta ne ake sa ran zabar gwarzon dan kwallon da yafi yin fice a Turai a bana a lokacin da za a raba jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai a Monaco.

Lionel Messi ne ya lashe kyautar a 2011 sannan Andres Iniesta ya dauka a 2012, a shekarar 2013 kuwa Frank Ribery aka zaba, yayin da Rolando ya lashe kyautar bara.

Ga sunayen 'yan wasa 10 da aka fitar:

  • Gianluigi Buffon (Italy - Juventus)
  • Eden Hazard (Belgium - Chelsea FC)
  • Lionel Messi (Argentina - FC Barcelona)
  • Paul Pogba (France - Juventus)
  • Andrea Pirlo (Italy - Juventus, New York City FC)
  • Cristiano Ronaldo (Portugal - Real Madrid CF)
  • Luis Suárez (Uruguay - FC Barcelona)
  • Carlos Tévez (Argentina - Juventus, CA Boca Juniors)
  • Arturo Vidal (Chile - Juventus)
  • Neymar(Brazil - Barcelona)