West Ham ta janye daga zawarcin Barton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan West Ham ne ke yin adawa da dauko Barton

West Ham ta janye daga cinikin Joey Barton kan ya buga mata tamaula, sakamakon zanga-zangar da magoya bayan kungiyar suka yi don kin dan wasan.

Barton wanda QPR ta kawo karshen kwantiragin da suka kulla da dan wasan a baya, an yi shirin zai koma West Ham ne a matakin wanda ba shi da kulob.

Magoya bayan West Ham ne suka soki komawar dan kwallon mai shekaru 32 a shafin sada zumunta, kan rigingimun da yake shiga.

Shugaban kungiyar ne David Gold ya tabbatar da cewar West Ham ta janye daga zawarcin Barton ta twitter.