Wilshere zai koma taka leda nan da mako biyu

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wenger ya ce Wilshere yana murmurewa.

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce dan wasan kungiyar Jack Wilshere zai koma taka leda nan da makonni biyu bayan jinyar raunin da ya yi a kafarsa.

Wilshere, mai shekaru 23, ya ji raunin ne a lokacin da yake yin atisaye ranar daya ga watan Agusta, kuma an yi tsammanin zai kwashe watanni biyu yana jinya.

Amma Wenger ya ce dan wasan zai murmure a cikin makonni hudu, kuma "a kan hakan ake".

A wani batu mai alaka da wannan, an yi wa dan wasan kungiyar, Tomas Rosicky tiyata a gwiwarsa, kuma zai yi jinyar sama da watanni biyu.

A lokacin da yake jawabi gabanin fafatawar da Arsenal za ta yi da Crystal Palace ranar Lahadi, Wenger ya ce: "Mun ce Jack zai kwashe makonni hudu yana jinya, yanzu yana mako na biyu, don haka yana kan hanya."

Dan wasan tsakiya na kungiyar Rosicky, mai shekaru 34, ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Jamhuriyar Czech a wasan da suka yi da Iceland na neman cancantar shiga gasar cin kofin Turai na shekarar 2016 a watan Yuni.