Bayelsa da Enyimba sun tashi 1-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Enyimba ce ta daya a kan teburi da maki 42, bayan da ta buga wasanni 23

Bayelsa United ta buga kunnen doki da Enyimba a gasar Premier wasan mako na 23 da suka yi ranar Asabar.

Enyimba ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Sikiru Kamal a minti na 27 da fara tamaula.

Daf da za a ta fi hutun rabin lokaci ne Bayelsa ta farke kwallo ta hannu Raphael Onwurebe.

Da wannan sakamakon Enyimba tana mataki na daya a kan teburi da maki 42, yayin da Bayelsa ke mataki na 19 da maki 22.

Abia Warriors kuwa doke El-Kanemi Warriors ta yi da ci daya mai ban haushi.

Ranar Lahadi za a ci gaba da wasannin makwo na 23:

  • Lobi Stars - Taraba FC
  • Nasarawa United FC - Heartland FC
  • Akwa United - Sharks FC
  • Enugu Rangers - Ifeanyi Uba
  • Sunshine Stars - Giwa FC
  • Warri Wolves - Dolphins FC
  • Kwara United - Wikki Tourists
  • Kano Pillars - Shooting Stars FC