Tottenham ta dauko Clinton N'Jie

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Clinton N'Jie ya bar buga gasar Faransa ya dawo Premier

Kungiyar Tottenham ta sayo dan kwallon Kamaru, Clinton N'Jie daga kulob din Lyon na Faransa.

Clinton N'Jie mai shekaru 22, ya saka hannu kan kwantiragin shekaru biyar, domin ya murza leda a White Hart Lane.

Dan wasan ya ci wa Lyon kwallaye bakwai a bara, sannan ya zura kwallaye shida a raga a wasanni 10 da ya buga wa Kamaru.

Tottenham ta dauko Clinton N'Jie ne, bayan da ta sayar da Roberto Soldado ga Villareal.