Andy Murray ya lashe Rogers Cup

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rabon da Murray ya doke Djokovic tun a 2013

Andy Murray ya lashe Rogers Cup a gasar kwallon tennis, bayan da ya doke Novak Djokovic a karon farko tun 2013.

Murray ya doke Djokovic ne da ci 6-4 da 4-6 da kuma 6-3 a cikin awa uku da suka fafata, kuma hakan ne ya bashi damar lashe kofi na hudu a shekarar nan.

Kuma nasarar da Murray ya yi a kan Djokovic wanda rabon da ya yi hakan tun a gasar Wimbledon ta 2013, zai kara masa kwarin gwiwar tunkarar US Open da za a fara ranar 31 ga watan Agusta a New York.

Haka kuma Murray din ya yi nasarar lashe gasar kwararru wato Masters karo na 11 kenan.