Chelsea ta dauko dan Ghana Baba Rahman

Rahman ya buga wa Augsburg wasanni 31 a kakar bara

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Rahman ya buga wa Augsburg wasanni 31 a kakar bara

Chelsea ta amince ta dauki Baba Rahman daga kulob din Augsburg dake buga Bundesligar Jamus.

Chelsea ce ta sanar da cimma yarjejeniyar dauko dan kwallon Ghana mai shekaru 21 a shafinta na Intanet, sai dai Augsburg ta ce kar a bayyana yawan kudin da aka yi cinikin.

Tun a baya aka dunga alakanta Chelsea da za ta dauko dan wasan domin ya maye gurbin Filipe Luis wanda ya koma Atletico Madrid da murza leda.

Mourinho wanda ya sha kashi a hannun Manchester City da ci uku da nema a gasar Premier ranar Lahadi ya ce kawo dan kwallon zai yi gogayya da Azpilicueta mai tsaron baya a bangaren hagu.

Rahman ya buga wa tawagar Ghana gasar cin kofin Afirka wanda Ivory Coast ta doke su a wasan karshe a watan Fabrairu.