Kano Pillars ta doke Shooting Stars 4-1

Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Kano Pillars ta koma mataki na hudu a kan teburi

Kano Pillars ta samu nasara a kan Shooting Stars da ci 4-1 a gasar Premier wasan makwo na 23 da suka kara ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Sunshine Star 4-0 ta casa Giwa FC, sai kuma Nasarawa United da ta doke Heartlanda da ci 2-0.

Wikki Tourist tattaki ta yi ta doke Kwara United har gida da ci daya mai ban haushi, yayin da IfeanyiUbah ma ta casa Rangers da ci 3-2 a Enugu.

Tun a ranar Asabar Bayelsa United da Enyimba suka tashi kunnen doki, a inda Abia Warriors ta samu nasara a kan El-Kanemi Warriors da ci daya mai ban haushi.

Sunshine Stars ta koma matakinta na daya a kan teburi da maki 43, sai Enyimba a matsayi na biyu da maki 42, Warri Wolves ta uku a da maki 40, Kano Pillars ta hudu da maki 37.

Ga sakamakon wasannin mako na 23 da aka yi:

  • Lobi Stars 2-1 FC Taraba
  • Nasarawa Utd 2-0 Heartland
  • Akwa Utd 3-1 Sharks
  • Rangers 2-3 FC Ifeanyiubah
  • Sunshine Stars 4-0 Giwa FC
  • Kwara Utd 0-1 Wikki Tourists
  • Kano Pillars 4-1 Shooting Stars
  • Warri Wolves 1-0 Dolphins
  • Bayelsa United 1-1 Enyimba
  • Abia Warriors 1-0 El-Kanemi