Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Shago na Kada Mutsa daga Arewa da Matawallen Kwarkwada daga Kudu, babu kisa a wannan wasan

An dambatawa a wasanni da dama a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja ranar Lahadi.

An fara ne da dambe tsakanin Shagon Shagon Lawwali daga Arewa da Shagon Kurari daga Kudu, kuma a turmin farko Shagon Lawwali ya yi kisa.

Dambe na biyu kuwa Shagon Soja daga Arewa ne ya buge Shagon Autan Faya daga Kudu, wasan gaba kuwa Garkuwan Autan Faya ne daga Kudu ya kashe Shagon Dogon Kyallu.

Bahagon Musan Kaduna kuwa daga Arewa wani irin kisa ya yi wa Shagon Audu na mai Kashi daga Arewa, domin da ya zo faduwa kansa ne ya tsake a kasa abin ban tausayi.

Autan Faya daga Kudu kuwa shigar sauri ya yi wa Dogon Shagon 'Yar Tasa daga Arewa, kuma nan da nan aka kai Dogon Shagon 'Yar Tasa kasa wanwar.

Fafatawa tsakanin Matawallen Kwarkwada daga Kudu da Shago na Kada Mutsa babu kisa, shi ma wasan Bahagon Mai Maciji daga Kudu da Sojan Kyallu daga Arewa ba kisa.

Damben Jirgi Bahago daga Kudu da Kurarin Kwarkwada turmi daya suka taka Sarkin Gida na Jafaru Kura ya raba wasan, bisa fasawa Kurari goshi da aka yi a turmin farko.

Shagon Shagon Alhazai daga Arewa doke Dogon Kurari ya yi daga Kudu, kuma sai da aka dauki mintuna hudu kafin Dogon Kurari ya farfado daga suman da ya yi.

Shagon Dogon Jango daga Kudu shi kuwa kashe Shagon Bahagon Sarka daga Kudu ya yi, sai dai Sarka ya yi korafin cewar kwashe masa kafafu Dogon Jango ya yi.