Muna kishirwar lashe kofi - Pellegrini

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Manchester City ta samu nasara a wasannin Premier biyu a jere a bana

Kocin Manchester City, Manuel Pellegrini ya ce suna kishirwar kofi da kuma takaicin da suka yi a bara na kasa kare kambunsu.

Manchester City ta kammala gasar Premier bara ne a mataki na biyu, biye da Chelsea wacce ta lashe kofin da tazarar maki takwas tsakani.

Da ya ke tattaunawa da 'yan jaridu bayan da City ta casa Chelsea 3-0 a gasar Premier ranar Lahadi, Pellegrini ya ce abin da ya faru a bara ya zama darasi a garesu.

Sergio Aguero ne da Vincent Kompany da kuma Fernandinho suka ci wa Manchester City kwallaye ukun da ta doke Chelsea a Ettihad.

City ta lashe wasanni biyu a jere a gasar Premier bana, hakan ne kuma ya sa ta dare mataki na daya a kan teburi da maki shida.

Ita kuwa Chelsea tana mataki na 16 a kan teburi da maki daya kacal.