Ramos ya sabunta kwantiragi a Madrid

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption United ta bukaci ta bai wa Madrid De Gea a bata Ramos a bana

Dan kwallon da Manchester United ta dade tana zawarci Sergio Ramos ya amince zai sabunta kwantiraginsa da Real Madrid zuwa shekaru biyar.

Ramos dan wasan Spaniya zai rattaba hannu a kan kunshi yarjejeniyar ne a gaban shugaban Madrid Florentino Perez ranar Litinin.

Tun a watan Yuni United ta taya Ramos kan kudi £28.6m, a inda Madrid ta ki sayar mata da dan wasan.

Ramos ya koma Madrid daga Sevilla a 2005, ya kuma buga wa Spaniya wasanni 128.

Dan wasan shi ne wanda ya fi dadewa yana buga wa Real Madrid tamaula, kuma Rafael Benitez ne ya nada shi kyaftin din kulob din a watan Yuli, bayan da Casillas ya koma Porto da murza leda