Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 41 Super Eagles

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun a baya Oliseh ya ce ya kagu ya fara nuna kwarewarsa a fagen horas da tamaula

Sabon kocin tawagar kwallon kafar Nigeria, Sunday Oliseh ya gayyaci 'yan kwallo 41, domin fuskantar Tanzania a Dar Es Salam.

Nigeria za ta kara da Tanzania ne a gasar neman gurbin shiga wasan cin kofin nahiyar Afirka da za su fafata ranar Asabar 5 ga watan Satumba.

Cikin 'yan wasan da ya gayyato 18 suna buga tamaula ne a Turai, sauran 23 suna murza leda ne a gasar Premier Nigeria.

Kocin na sa ran dukkan 'yan wasan da ya gayyato za su halarci sansanin atisaye dake Abuja nan da ranar 31 ga watan Agusta.

Ga jerin 'yan wasan dake wasa a Turai da Oliseh ya gayyata:

Masu tsaron raga: Vincent Enyeama (Lille OSC, France); Carl Ikeme (Wolverhampton Wanderers, England)

Masu tsaron baya: Leon Balogun (FSV Mainz 05, Germany); Kingsley Madu (AS Trencin, Slovakia); Godfrey Oboabona (Caykur Rizespor, Turkey); William Troost Ekong (FK Haugesund, Norway); Kenneth Omeruo (Kasimpasa SK, Turkey)

Masu wasan tsakiya: Joel Obi (Torina FC, Italy); Izunna Ernest Uzochukwu (FC Amkar Perm, Russia); Obiora Nwankwo (Coimbra FC, Portugal); Lukman Haruna (Anzhi Machatsjkala, Russia); Rabiu Ibrahim (AS Trencin, Slovakia)

Masu zura kwallo a raga: Ahmed Musa (CSKA Moscow, Russia); Emem Eduok (Esperance ST, Tunisia); Emmanuel Emenike (Al Ain, UAE); Anthony Ujah (Werder Bremen, Germany); Sylvester Igboun (FC UFA, Russia); Moses Simon (KAA Gent, Belgium)