Sunshine ta dare teburin gasar Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto sunshinestarstwitter
Image caption Sunshine Stars ta hada maki uku a ranar Lahadi

Sunshine Stars ta hau kan teburin gasar Premier, bayan da ta doke Giwa FC da ci 4-0 a gasar Premier wasan mako na 23 da ta yi a jiya Lahadi.

Sunshine din tana da maki 43 jumulla, bayan wasanni 23 a gasar, sai Enyimba a mataki na biyu da maki 42, Warri Wolves da maki 40 a matsayi na uku, yayin da Pillars ke da maki 39 kuma ta hudu a kan teburin.

Sharks tana mataki na 17 da maki 24, sai Dolphins da maki 21 a matsayi na 18, Bayelsa ta 19 da maki 21, sai Taraba FC ta karshe a teburi da maki 19.

Tunde Adeniji ne na Sunshine Stars ke kan gaba wajen yawan cin kwallaye a gasar, a inda ya zura 12, sai kuma Bright Ejike na Heartland da ya ci kwallaye 11 a gasar.

'Yan wasa uku ne suka ci kwallaye tara-tara a Premier da suka hada da Esosa Igbinoba na Nasarawa United da Gbolahan Salami na Warri Wolves da kuma Chisom Chikatara na Abia Warriors.