An raba jan kati 37 a gasar Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto thenff
Image caption Ranar Laraba za a shiga gasar makwo na 24

Alkalan gasar Premier Nigeria sun bayar da katin gargadi 815, haka kuma sun kori 'yan wasa daga fili sau 37, bayan da aka kammala wasannin makwo na 23 a ranar Lahadi.

Jumulla an buga wasannin 230 kuma Sunshine Stars ce ta daya a kan teburi da maki 43, sai Enyimba a mataki na biyu da maki 42, Warri Wolves da maki 40 a matsayi na uku, yayin da Pillars ke da maki 39 kuma ta hudu a kan teburin.

Sharks tana mataki na 17 da maki 24, sai Dolphins da maki 21 a matsayi na 18, Bayelsa ta 19 da maki 21, sai Taraba FC ta karshe a teburi da maki 19.

Tunde Adeniji ne na Sunshine Stars ke kan gaba wajen yawan cin kwallaye a gasar, a inda ya zura 12, sai kuma Bright Ejike na Heartland da ya ci kwallaye 11 a gasar.

'Yan wasa uku ne suka ci kwallaye tara-tara a Premier da suka hada da Esosa Igbinoba na Nasarawa United da Gbolahan Salami na Warri Wolves da kuma Chisom Chikatara na Abia Warriors.