Real Madrid ta dauki Mateo Kovacic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Laraba za a gabatar da Kovacic gaban magoya bayan Real Madrid

Real Madrid ta kammala sayo dan kwallon Inter Milan, Mateo Kovacic mai buga wasan tsakiya, sai dai ba ta bayyana kudin da ta dauko dan wasan ba.

Kovacic mai shekaru 21, dan kwallon tawagar Croatia ya saka hannu kan kwantiragin shekaru shida a Bernabeu, kuma za a gabatar da shi a gaban magoya bayan kungiyar ranar Laraba.

Dan wasan ya ci kwallaye takwas a fafatawa 97 da ya yi wa Inter, tun komawarsa kulob din daga Dinamo Zagreb a 2013.

Kovacic wanda ya buga wa Crotia wasanni 21, zai murza leda a Madrid tare da abokin da suke takawa kasarsu tamaula Luka Modric.

Real Madrid za ta fara buga wasan gasar La Ligar bana a ranar Lahadi, a inda za ta yi gumurzu da Sporting Gijon.