Enyimba ta samu nasara kan Kano Pillars

Hakkin mallakar hoto enyimba twitter
Image caption Enyimba ta dare mataki na daya a kan teburin Premier da maki 45

Enyimba ta doke Kano Pillars da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 24 da suka buga a Aba ranar Laraba.

Enyimba ta ci kwallon ne daga bugun fenariti a minti na 28 da fara tamaula, kuma Ifeanyi George ne ya zura kwallon a raga.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Wikki Tourist ta zura kwallaye 2-0 a ragar Abia Warriors, yayin da El-Kanemi Warriors da Warri Wolves suka tashi wasa babu ci.

Heartland kuwa doke Kwara United ta yi da ci daya mai ban haushi, itama Dolphins 1-0 ta samu nasara a kan Sunshine Stars, kuma fafatawa tsakanin FC Taraba da Bayelsa United suka tashi kowa yana nema.

Za a karasa sauran wasannin makwo na 24 ranar Alhamis tsakanin Sharks da Lobi Stars da kuma karawa tsakanin Ifenyiubah da Akwa United.

Giwa FC za ta karbi bakuncin Enugu Rangers a Jos, sai kuma Nasarawa United da za ta ziyarci Shooting Stars.

Ga sakamakon wasan makwo na 24 da aka buga:

  • El-Kanemi 0-0 Warri Wolves
  • FC Taraba 0-0 Bayelsa United
  • Dolphins 1-0 Sunshine Stars
  • Wikki Tourists 2-0 Abia Warriors
  • Heartland 1-0 Kwara United