An dakatar da Pique daga buga wasanni hudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pique ya nemi afuwa kan jan katin da aka yi masa, amma ya karyata zargin da ake yi masa

Hukumar kwallon kafar Spaniya ta dakatar da mai tsaron bayan Barcelona, Gerard Pique daga buga wasanni hudu, bisa zargin cin zarafin mataimakin alkalin wasa da ya yi.

An ce Pique ya fadi munanan kalamai kan mataimakin alkalin wasa a lokacin da aka ba shi jan kati a karawar da Barcelona ta tashi kunnen doki da Athletico Bilbao a wasan Super Cup na Spaniya.

Dan wasan na tawagar Spaniya ya nemi afuwa ta Twitter kan halayyar da ya nuna, sai dai bai amince da cewar ya fadi kalaman cin zarafi ga mataimakin alkalin wasan ba.

Barcelona ba ta ce komai ba kan hukuncin da aka yanke wa Pique, kuma ko za ta daukaka kara ko akasin hakan.

Barca za ta fara kare kofin La Liga na bara da ta dauka, a inda za ta fafata da Ahtletico Bilbao ranar Lahadi.