Saliyo za ta kara da Ivory Coast a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rukunin ya kunshi Saliyo da Sudan da Gabon da Ivory Coast

Tawagar kwallon kafar Saliyo za ta kara da ta Ivory Coast a wasan neman gurbi a gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar 6 ga watan Satumba a Nigeria.

Kasashen biyu za su fafata ne a Legas, bayan da aka hana Saliyo karbar bakuncin manyan wasannin tamaula, saboda barkewar cutar Ebola a kasar.

A gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala a watan Fabrairu, Saliyo ta buga wasanni biyu na neman shiga gasar da Ivory Coast a Abidjan, amma ta kasa samun izinin taka leda a wata kasar.

A wannan watan ne aka dauke takunkumin hana taka leda a gasar kasar ta Saliyo.

Hukumar kwallon kafar jihar Legas ce za ta samar da abubuwan da za a bukata a lokacin wasan a filin Teslim Balogun har da kayayyakin kula da lafiya.