Zan koma kan ganiya ta — Rooney

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rooney ya ce yana shan suka bisa rashin katabus dinsa.

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya ce zai koma kan ganiyarsa ta zura kwallaye bayan ya sha suka bisa rashin katabus tun da aka fara kakar wasan Premier Ingila ta bana.

Rooney, mai shekaru 29, ya taka leda a matsayin babban dan wasan da ke cin kwallo amma ya kasa zura kwallo a wasansu na farko, kuma hakan ya sa wasu na cewa dan wasan ba shi da anfani yanzu.

Dan wasan ya ce ya yi wuri a fara sukarsa, yana mai cewa zai yi bakin kokarinsa wajen inganta yadda yake taka leda.

Rooney ya ce : "Na buga wasa daya mara armashi amma kowa sai suka ta yake yi. Tun da na fara kwallon kafa nake shan suka amma ina fatan a zan zura kwallo a fafatawar da za mu yi a karshen mako."

Kociyan United Louis van Gaal ya bari 'yan wasan gaba Robin van Persie da Radamel Falcao sun koma wasu kungiyoyin a lokacin bazara, lamarin da ya sa yanzu Rooney da Javier Hernandez da James Wilson ne kawai 'yan wasansa da za su iya zura kwallo.