'Mikel na son ya bugawa Super Eagles'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mikel ya bugawa Nigeria wasa a gasar cin kofin duniya

Wakilin dan kwallon Chelsea, John Mikel Obi watau John Shittu ya ce dan wasan na son ya ci gaba da murzawa kasar leda duk da cewar ba a gayyace shi ba a wasan da Super Eagles za ta buga a watan Nuwamba.

Sabon Kocin Nigeria Sunday Oliseh ya ce bai gayyaci Mikel ba saboda bai san yadda zai sami dan wasan ba.

Amma dai Shittu ya shaidawa BBC cewar "Mikel ba zai taba juyawa Nigeria baya ba."

A ranar Alhamis ne, Oliseh ya bayyana cewar bai gayyaci Mikel ba saboda ya ki amsa wayarsa a lokacin da ya je rangadi a Ingila.

"Na je Ingila a farkon wannan watan na kira wayar Mikel sau hudu babu amsa. Na aiki masa sako babu amsa," in ji Oliseh.