Zabaleta zai yi jinyar wata guda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zabaleta ya dade yana haskakawa a Etihad

Dan kwallon Manchester City, Pablo Zabaleta zai yi jinyar a kalla wata guda bayan da ya ji rauni a gwiwarsa a lokacin horo.

Dan Argentina mai shekaru 30, bai buga wasanni biyu na farko ba a gasar Premier ta Ingila tare da City.

Watakila kuma ba zai buga wasanni shida ba kuma Bacary Sagna ne zai maye gurbinsa.

"Pablo Zabaleta na da matsala a gwiwarsa," in ji Manuel Pellegrini.

A wannan makon dai Gael Clichy da Fabian Delph suka koma horo bayan 'yar jinyar da suka yi.