Barcelona za ta fara La Liga ranar Lahadi

Ranar Lahadi Barcelona da Real Madrid za su fara buga wasan farko a La Ligar bana

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ranar Lahadi Barcelona da Real Madrid za su fara buga wasan farko a La Ligar bana

Barcelona za ta fara kare kofin La Liga na bara da ta lashe a kakar wasannin bana ranar Lahadi.

Barcelona za kara ne da Ahletico Bilbao wacce ta doke ta 5-1 gida da waje a wasan Spanish Super Cup.

Barca ta yi rashin 'yan wasan a bana da suka bar kungiyar da suka hada da Pedro wanda ya koma Chelsea sai Xavi da ya koma Qatar taka leda a kungiyar Al Sadd.

'Yan wasa biyu da Barca ta sayo Arda Turan da Aleix Vidal ba za su fara buga mata wasa ba sai a watan Janairu, saboda hukunta kungiyar da aka yi kan karya ka'idar cinikayyar 'yan wasa kasa da shekaru 18.

Real Madrid kuwa karkashin sabon koci Rafeal Benitez za ta fara yin nata wasan ne a waje, a inda za ta jiyarci Sporting Gijon.

Madrid wacce ta kammala a mataki an biyu a gasar La Ligar bara ta sayo 'yan wasa a bana kuma fitattu daga cikin su sun hada da Danilo daga Porto da kuma Mateo Kovacic daga Inter Milan.