United ta tashi wasa da Newcastle 0-0

Image caption United za ta kara da Club Brugge ranar Laraba a wasa na biyu na gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai

Manchester United ta tashi karawa tsakaninta da Newcastle babu ci a gasar Premier wasan makwo na uku da suka yi a Old Trafford.

United ta fara wasan da kai matsi har sai da Rooney ya zura kwallo a raga, amma alkalin wasa ya ce ya yi satar gida.

Haka ita ma Newcastle ta kai kora da dama musamman ta wajen Aleksandar Mitrovic.

Da wannan sakamakon United da Newcastle sun rabi maki daya-daya tsakaninsu, kuma jumulla United tana da maki bakwai, Newcastle na da maki biyu, bayan wasanni uku da suka buga a gasar.

Newcastle United za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na hudu, yayin da Manchester United za ta ziyarci Swansea.