Chelsea ta sayo dan kwallon Brazil Kenedy

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce mai rike da kofin Premier da ta dauka a bara

Kungiyar Chelsea ta sayo dan kwallon Brazil, Kenedy mai shekaru kasa da 20 daga kulob din Fluminense.

Kenedy mai shekaru 19 yana daga cikin matasan 'yan wasan da suka yi wa Chelsea wasannin atisaye a kudancin Amurka, sai yanzu ne ya kammala komawa Stamford Bridge da murza leda.

Dan wasan ya ce abu ne mai mahimmaci a rayuwarsa ta kwallon kafa da ya koma gasar Premier, yana kuma fatan zai zama fitatcen dan wasa a Chelsea.

Kenedy zai taka leda a Chelsea tare da 'yan wasan Brazil da suka hada da Ramires da Oscar da Willian, bayan da Nathan ya koma Vitesse Arnhem aro ta Netherlands.