United ba ta bukatar mai zura kwallo a raga

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rabon da Rooney ya ciwa United kwallo tun Afirilu

Kocin Manchester United, Louis van Gaal ya ce kungiyar ba ta bukatar sayo dan wasa mai zura kwallo a raga domin karfafa wasannin da take yi.

Van Gaal ya fadi hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin 'yan jaridu, bayan da suka tashi wasa babu ci da Newcastle United ranar Asabar a Old Trafford a wasan Premier.

Kwallaye biyu kacal United ta ci a wasannin Premier uku da ta buga, kuma rabon da Wayne Rooney ya ciwa United kwallo tun ranar 4 ga watan Afirilu.

United ta yi zawarcin Pedro na Barcelona kafin daga baya ya amince ya buga wa Chelsea tamaula maimakon ya murza leda a Old Trafford.

Van Gaal ya kara da cewar United ba sai ta sayo dan wasa mai zura kwallo a raga ba, domin kungiyar tana da kwari.

United ta barar da damarmakin zura kwallo a raga a karawar da ta yi da Newcastle United, har ma Rooney ya ci kwallo amma alkalin wasa ya ce an yi satar gida.