Balotelli zai koma AC Milan da taka leda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Balotelli na fatan ya dawo da tagomashinsa a AC Milan

Dan kwallon Liverpool, Mario Balotelli ya amince da a zabtare masa albashi, domin ya koma murza leda aro a tsohuwar kungiyarsa AC Milan.

Kwallo daya kacal Balotelli ya ci wa Liverpool a gasar Premier, tun lokacin da ta sayo shi daga Milan din kan kudi £16m a watan Agustan 2014.

Liverpool din ba ta tafi da dan kwallon wasannin gwaji da ta yi kafin tunkarar gasar bana ba, sannan kuma shi kadai yake yin atisaye ba tare da 'yan wasa ba.

Tuni kuma Liverpool din ta sayo Christian Benteke da Roberto Firmino da kuma Danny Ings a bana, yayin da Divock Origi ya dawo Anfield, bayan da ya buga wa Lille wasanni aro.