Ban aikata ba dai-dai ba a Fifa - Blatter

Image caption A watan Fabrairu Sepp Blatter zai bar jagorancin Fifa

Mai shirin barin kujerar shuganacin Fifa, Sepp Blatter ya shaidawa BBC cewar ba shi da hannu kan zargin cin hanci da rashawa a harkar kwallon kafa.

Blatter wanda ya fara shugabantar Fifa a 1998, zai sauka daga jan ragamar hukumar a watan Fabrairu, saboda zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye manyan jami'an hukumar.

Shugaban wanda aka zaba karo na biyar a watan Mayu domin ya jagoranci hukumar, ya amince zai yi murabus bisa badakalar da ta mamaye Fifa.

Blatter ya ce "Na yi hakan ne domin ya kare martabar Fifa, da kuma ni kaina, na kuma san dukkan abubuwan dana aikata a hukumar, kuma ni mai gaskiya ne, ba ni da laifi".

Ana cigaba da gudanar da bincike biyu kan cin hanci da rashawa a Fifa, bayan da aka kama manyan jami'an hukumar bakwai a watan Mayu a taron hukumar.

A hirar da Blatter ya yi da BBC ya ce babu cin hanci a hukumar, kuma babu cin hanci a kwallon kafa, illa dai akwai cin hanci a tattare da mutane.