Ramsey ya bayar da shawara a tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal za ta ziyarci Newcastle a ranar Asabar a wasan Premier makwo na hudu

Aaron Ramsey ya bukaci a wasan kwallon kafa a kwaikwayi ta zari-riga wajen kafa na'urar bidiyo da za ta nuna abun da ya faru a lokacin da ake buga tamaula.

Ramsey ya fadi haka ne saboda kwallon da ya ci Liverpool a wasan gasar Premier da suka buga ranar Litinin, amma alkalin wasa ya hana kwallon da cewar an yi satar gida.

Da aka maimaita abin da ya faru a akwatin talabijin, dan wasan bai yi satar gida ba a karawar da suka tashi wasan babu ci a Emirates.

Mahukuntan wasan kwallon zari-ruga sukan sake kallon wasa ta na'urar bidiyo nan take a duk lokacin da aka ci karo da takaddama a lokacin da ake wasa.

Bayan kammala wasan, Arsene Wenger ya ce mataimakin alkalin wasa Simon Bennett ya yi kuskure kan hukuncin da ya yanke cewar an yi satar gida.

Masu tsara dokokin kwallon kafa na kungiyar masu buga tamaula ta duniya ta jingine batun gwada fasahar bidiyo a filin wasa da shekara daya a taron da suka yi a watan Fabrairu.