Cuadrado na daf da komawa Juventus

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Chelsea tana mataki na 10 a kan teburin Premier

Dan kwallon Chelsea, Juan Cuadrado na daf da komawa Serie A da taka leda a kulob din Juventus.

Cuadrado dan kwallon Colombia wanda ya koma Chelsea kan kudi £23.3m daga Fiorentina a Fabrairu, zai buga wa Juventus wasa aro zuwa karshen kakar bana.

Dan wasan mai shekaru 27 ya buga wa Chelsea wasanni 15, hudu daga ciki da shi aka fara tamaula.

Tuni Chelsea ta sayo Pedro daga Barcelona kan kudi £21.1m a ranar Alhamis.