Everton ta amince Stone ya bar kungiyar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Everton ta yi rashin nasara a hannun Manchester City har gida a gasar Premier ranar Lahadi

Everton ta amince da mai tsaron bayanta John Stone ya bar ta, bayan da Chelsea ta nace sai ta sayi dan wasan.

Chelsea ta fara taya Stone kan kudi £20m da kuma £26m sannan ta kara tayi na uku kan kudi da ya kai £30m.

Everton ta ci gaba da nanata cewar ba za ta sayar da dan kwallon ba a bana, kuma kungiyar ta ki cewa komai kan bukatar da Chelsea ta gabatar mata.

Stone ya koma Everton ne daga Barnsley a watan Fabrairun 2013 kan kudi £3m.