An gama duba lafiyar Balotelli a AC Milan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana mataki na uku a kan teburin Premier da maki bakwai

Likitocin AC Milan sun kammala duba lafiyar Mario Baloteli a shirin da yake yi na komawa can da murza leda aro.

Balotelli ya amince a rage masa albashi domin ya sake buga wa Milan din kwallo, kuma Liverpool za ta dinga biyan wani kaso na albashin dan wasan.

Dan kwallon dan Italiya zai buga wa Milan wasanni karo na biyu, har ma ana sa ran zai taka leda a wasan da kulob din zai kara da Empoli a a gasar Serie A ranar Asabar.

Kwallo daya kacal Balotelli ya ci wa Liverpool a gasar Premier, tun lokacin da ta sayo shi daga Milan din kan kudi £16m a watan Agustan 2014.