An ci kwallaye 533 a gasar Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An buga wasannin makwo na 25 a gasar Premier

An zura kwallaye 533 daga cikin wasanni 246 da aka buga a gasar Premier Nigeria tun lokacin da aka fara gasar.

Tunde Adeniji na Sunshine Stars shi ne ke kan gaba a matsayin wanda yafi cin kwallaye a gasar a inda ya zura 13 a raga.

Dan wasan Heartland Bright Ejike shi ne ke matsayi na biyu da kwallaye 11, yayin da Gbolahan Salami na Warri Wolves da kuma Chisom Chikatara na Abia Warriors kowannensu ya ci kwallaye 10 a gasar.

'Yan wasa uku ne suka ci kwallaye tara-tara a gasar da suka hada da Esosa Igbinoba na Nasarawa Utd da Anthony Okpotu na Lobi Stars da kuma Prince Aggreh na Sunshine Stars.

Enyimba ce ke kan gaba a kan teburin da maki 48, sai Sunshine Stars da maki 46 a matsayi na biyu, Warri Wolves ta uku da maki 44, Kano Pillars tana mataki na 6 da maki 37.