Kamaru ta gayyaci Bassong da Matip

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamaru za ta kara da Gambia a ranar 6 ga watan Satumba

Hukumar kwallon kafar Kamaru ta ce ta gayyato Sebastien Bassong da kuma Joel Matip cikin tawagar 'yan wasan da za su kara da Gambia a watan Satumba.

Kamaru za ta kara da Gambia ranar 6 ga watan Satumba a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2017.

Bassong wanda ke taka leda a Norwich bai buga wa Kamaru gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil a 2014 ba, shi kuwa Matip mai wasa a Schalke rabon da ya yi wa Indomitable wasa tun kammala gasar kofin duniyar.

Kocin Kamaru, Volker Finke ya gayyaci 'yan wasa 23 da za su fafata a wasan da za su buga karo na biyu a rukuni na 13.

A watan yuni daya da nema Kamaru ta doke Mauritania a wasan farko da ta yi a cikin rukunin.

Finke ya kuma kira matashin dan wasa Andre Onana mai shekaru 19 dake tsaron raga a Ajax da kuma Felix Eboa Eboa wanda ke murza leda a karamar kungiyar Paris Saint-Germain.