Masar ta fice daga wasannin Afirka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara wasannin ranar 6 zuwa 18 ga watan Satumba

Masar ta fice daga wasan kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekaru 23 a gasar wasannin Afirka da za a yi a Brazzaville.

Masar din ta ce ta janye tawagar kwallon kafa ta mata da kuma ta maza daga shiga wasannin Afirka da za a fara tsakanin 6 zuwa 18 ga watan Satumba.

A dokar gasar ta ce kwamitin tsara wasannin za su iya maye kasar da ta janye da wacce kasar da ta janye ta fitar a wasannin neman gurbin shiga gasar.

Sai dai kuma Senegal ta ce ba za ta iya tura tawagar mata domin maye gurbin Masar ba, haka ma Burundi ta ce da wuya ta tura tawagar kwallon kafar maza gasar, a inda suka ce an sanar da su a kurarren lokaci.

Ga jadawalin rukunnan da aka raba a gasar.

Mata

Group A - Congo, Nigeria, Tanzania, Cote d'Ivoire

Group B - Cameroon, Ghana, South Africa

Maza

Group A - Congo, Sudan, Zimbabwe, Burkina Faso

Group B - Ghana, Senegal, Nigeria.