United ta samu tikitin shiga Champions League

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau uku Manchester United tana lashe kofin zakarun Turai a tarihi

Manchester United ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai na bana, bayan da ta doke Club Brugge da ci 4-0 a wasan neman gurbin shiga gasar da suka kara ranar Laraba.

Wayne Rooney ne ya ci kwallaye uku rigis a wasan, yayin da Ander Herrera ya kara ta uku minti na 18 da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

A wasan farko da suka buga a Old Trafford, United ce ta doke Brugge da ci 3-1, kuma jumulla ta ci kwallaye 7-1 kenan haduwa da suka yi gida da waje.

United za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai a bana, bayan da ta kasa samun tikitin shiga gasar bara, bisa kammala gasar Premier da ta yi a matsayi na bakwai a baran.

Kungiyoyin da za su wakilci Ingila a gasar sun hada da Chelsea wacce ta dauki kofin Premier bara da Manchester City da Arsenal da kuma Manchester United.

Ranar Alhamis za a raba jadawalin fara gasar cin kofin zakarun Turai na bana.