Fellaini zai koma gurbin mai cin kwallo a United

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United ce ta doke Club Brugge a Old Trafford a wasan farko da suka yi

Kocin Manchester United, Louis van Gaal ya ce zai mayar da Marouane Fellaini mai cin kwallo a kungiyar maimakon mai buga tsakiya a tamaula.

Fellaini ya shiga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai da United ta doke Club Brugge 3-1 daga baya ya kuma ci kwallo a karawar.

Van Gaal ya ce "Fellaini zai koma buga lamba tara ko kuma 10 a wasa, maimakon lamba shida ko takwas da yake yi a United".

A wasa na biyu da United za ta kara da Club Brugge ranar Laraba, mai tsaron ragarta David De gea ba zai buga mata wasan ba.

United ta kara karfin gurbin 'yan wasan da suke buga mata tsakiya a inda ta sayo Morgan Schneiderlin da kuma Bastian Schweinsteiger a bana.