Kungiyoyi 5 ne za su wakilci Spaniya a Champions League

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karon farko da kungiyoyi 5 za su wakilci kasa a gasar cin kofin zakarun Turai

Spaniya ta zama kasa ta farko da kungiyoyin kwallon kafarta biyar za su wakilce ta a gasar cin kofin zakarun Turan bana.

Valencia ta samu gurbin shiga gasar bana ne bayan da ta yi nasara a kan Monaco a wasan cike gurbin shiga gasar da ci 3 da 4 a wasan da suka yi gida da waje.

Sevilla ma tana daga cikin kungiyoyi da za su wakilci Spaniyar bayan da ta lashe Europa League na bara.

Kungiyoyin da za su wakilci kasar sun hada da Barcelona wacce ta dauki kofin La Liga na bara da Real Madrid wacce ta yi ta biyu a gasar da kuma Atletico wacce ta kammala gasar a mataki na uku.

Ranar Alhamis ne za a yi jadawalin fara gasar cin kofin zakarun Turai na bana.

Wannan shi ne karon farko da kungiyoyi biyar daga kasa daya za su buga gasar cin kofin zakarun Turai da kungiyoyi 32 ke fafatawa a gasar.

Kungiyoyin Spaniya sun lashe kofunan gasar zakarun Turai hudu daga cikin na kakar wasanni bakwai da aka yi a baya.