Bolt ya lashe tseren mita 200 a Beijing

Image caption Bolt ya ci gaba da kafa tarihi a fagen tsere a duniya

Dan kasar Jamaica Usain Bolt ya doke Justin Gatlin inda ya lashe tseren mita 200 a gasar wasanni da ke gudana a birnin Beijing na China.

Bolt mai shekaru 29, ya lashe tseren a cikin dakikoki 19.55 a yayinda dan Amurka, Gatlin ya zo na biyu a cikin dakikoki 19.74.

"Ina alfahari na wannan nasarar kuma na ji dadi kasancewa zakara a wannan gasar," in ji Bolt.

Dan Afrika ta Kudu, Anaso Jobodwana ne ya zama na uku a yayinda dan Biritaniya Zharnel Haughes ya zama na biyar.

A karshen mako ma, Usain Bolt din ya lashe tseren mita 100 a gasar.