Rarraba kungiyoyi a Gasar Zakarun Turai

Rabe-raben kungiyoyi a Gasar Zakarun Turai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea za ta kara a Rukunin G da Porto, wacce Mourinho ya jagorance ta lashe gasar a 2004

An rarraba kungiyoyi zuwa rukuni-rukuni domin fafatawa a zagayen farko na Gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Rabe-raben na nuni da cewa Arsenal za ta kara da Bayern Munich a Gasar cin Kofin Zakarun Turai a karo na uku a cikin kakar wasanni hudu a matakin na wasannin rukuni.

Ita kuma Manchester United, wacce ke kome wa gasar, za ta kara ne da PSV Eindhoven; ke nan dan wasanta na gaba, Memphis Depay zai kara da tsohon kulob dinsa.

Chelsea kuwa za ta kara da Porto, wacce Jose Mourinho ya jagorance ta ta lashe gasar a shekarar 2004.

Ga dai yadda rukunonin suke:

  • Rukunin A: Paris St Germain, Real Madrid, Shakhtar Donetsk, Malmo
  • Rukunin B: PSV Eindhoven, Manchester United, CSKA Moscow, VfL Wolfsburg
  • Rukunin C: Benfica, Atletico Madrid, Galatasaray, Astana
  • Rukunin D: Juventus, Manchester City, Sevilla, Borussia Monchengladbach
  • Rukunin E: Barcelona, Bayer Leverkusen, AS Roma, BATE Borisov
  • Rukunin F: Bayern Munich, Arsenal, Olympiakos, Dinamo Zagreb
  • Rukunin G: Chelsea, Porto, Dynamo Kiev, Maccabi Tel-Aviv
  • Rukunin H: Zenit St Petersburg, Valencia, Olympique Lyon, Gent

Karin bayani