Kevin de Bruyne ya ziyarci Man City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kevin De Bruyne ya yi wasa a Chelsea kafin ya koma Wolfsburg

Likitocin Manchester City na daf da duba koshin lafiyar Kevin de Bruyne a shirin da yake yi na koma can da murza leda.

Tuni aka kawo karshen takaddamar da ta hana dan wasan Belgium mai wasa a Wolfsburg koma wa Ingila da taka leda.

Ana hasashen cewa City za ta sayi De Bruyne kudin da ya dara wanda ta sayo Raheem Sterling £49m daga Liverpool a watan Yuli.

Dan wasan bai buga wa Wolfsburg gasar Bundesliga ranar Juma'a da ta kara da Schalke 04 ba.

Tsohon dan kwallon Chelsea, De Bruyne zai zamo dan wasa na biyu da aka saya mafi tsada a Ingila, bayan Angel Di Maria daga Real Madrid zuwa Manchester United a 2014.

De Bruyne ya koma taka leda Wolfsburg a watan Janairun 2014 daga kungiyar Chelsea.