Markovic ya koma Fernerbahce da taka leda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasannin Premier 11 Markovic ya buga wa Liberpool a bara

Dan kwallon Liverpool, Lazar Markovic ya koma Fernerbahce ta Turkiya da murza leda aro zuwa karshen kakar bana.

Markovic wanda Liverpool ta sayo daga Benfica a bara, ta amince ya je ya buga wasa aro da nufin ya kara samun gogewa a fagen tamaula.

Dan wasan ya buga wa Liverpool wasannin Premier 11 a kakar wasan bara, sannan kuma ya yi wa tawagar kwallon kafar Serbia wasanni 34.

Haka kuma Liverpool ta bayar da Mario Balotelli aro ga AC Milan, a inda take fatan Milan din za ta sayi dan kwallon idan ya taka rawar gani a Italiyan.