De Bruyne ya koma Man City da taka leda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasanni uku De Bruyne ya yi a Chelsea daga baya ya koma Wolfsburg

Manchester City ta kammala sayen dan kwallon Belgium mai wasa a Wolfsburg, Kevin De Bruyne kan kudi £55m.

De Bruyne mai shekaru 24 ya amince da yarjejeniyar shekaru shida a Ettihad, kuma shi ne babban dan kwallo da City ta sayo na hudu a bana, bayan Raheem Sterling da Fabian Delph da Nicolas da kuma Otamendi.

Haka kuma shi ne dan kwallo na biyu da aka saya mafi tsada a Ingila, bayan da United ta dauko Angel Di Maria kan kudi £59.7m daga Real Madrid.

De Bruyne wanda zai saka riga mai lamba 17 a Ettihad, ya koma Wolfsburg a watan Janairun 2014 daga Chelsea kan kudi £16.7m.