Horo da Shagon Mada sun dambata a Abuja

Image caption Horo daga Arewa da Shagon Mada daga Kudu, babu kisa a wannan takawar da suka yi

A ci gaba da damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria, an fafata a wasanni da dama ranar Lahadi.

An kara tsakanin Shagon Musan Kaduna daga Arewa da Autan Faya daga Kudu, kuma turmi uku suka yi babu kisa aka raba wasan.

Shi kuwa Bahagon Sisco daga Kudu kisa ya sha a hannun Dogon Jango a turmi na biyu kuma a cikin ruwan sanyi.

Bahagon Alin Tarara ma daga Arewa kashe Bahagon Sarka daga Kudu ya yi ba tare da ba ta lokaci ba kuma a turmi na biyu.

Damben Sanin Kwarkwada daga Kudu da Abban Nabacirawa turmi uku suka yi babu kisa Sarkin gida na Jafaru Kura ya raba damben.

Karawa ma tsakanin Jirgi Bahago daga Arewa da Alin Kwara daga Kudu babu wanda ya yi nasara a wasan aka kuma raba su bayan turmi uku da suka yi.

Nan da nan aka sa zare tsakanin Sarkin Dambe Ashiru Horo daga Arewa da Sarkin Dambe Shagon Mada daga Kudu, kuma turmi daya suka taka duk da babu kisa a wasan aka tashi daga kallo.