Manchester United na daf da daukar Martial

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United na son kara karfin gurbin masu zura mata kwallaye a raga

Manchester United na kokarin kammala cinikin dan kwallon Monaco Anthony Martial wanda take son saya kan kudi £36m.

Monaco ta bai wa Martial mai shekaru 19, wanda Arsenal ta dade tana zawarci izinin ya je Old Trafford domin a duba koshin lafiyarsa a ranar Litinin.

Dan wasan ya ci kwallaye takwas daga wasanni 31 da ya yi a gasar Faransa wato Ligue 1 a bara.

Idan har United ta sayi Martial zai zamo dan wasa na uku da kungiyar ta dauka mafi tsada a tarihi, bayan Angel Di Maria da ta biya £59.7m da kuma Juan Mata kan kudi £37.1m.

Dan wasan ya fara murza leda a Lyon a matsayin kwararren dan wasa a watan Disambar 2012, daga nan ya koma Monaco da taka leda a watan Yunin 2013.