Ana sa ran Hernandez zai koma Bayer Leverkusen

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hernandez ba ya buga wasanni akai-akai a Manchester United

Ana kyautata cewar Javier Hernandez zai koma murza leda Bayer Leverkusen, hakan kuma zai kawo karshen shekaru biyar da ya yi a Old Trafford.

Hernandez dan kwallon Mexico ya zauna a kan benci a lokacin da Swansea ta doke United da ci 2-1 a wasan Premier ranar Lahadi.

Dan wasan ya ci kwallaye 59 daga wasanni 156 da ya buga wa United tun lokacin da ya bar Chivas de Guadalajara a 2010.

Hernandez ya buga tamaula aro kusan kakar bara gabaki daya a Real Madrid a bara, har ma an sa ran Madrid din za ta dauki dan kwallo.

Haka kuma wani rahoton na cewa Adnan Januzaj zai koma Borussia Dortmund da taka leda daga United din aro.

Kuma tuni mai tsaron ragar United Anders Lindegaard ya isa West Brom a inda likitocin kulob din ke duba lafiyarsa domin komawa can da murza leda.