Nigeria ta lashe gasar Kwallon Kwando

Hakkin mallakar hoto FIBAAFRICA
Image caption Wanne ne karon farko da Najeriya ta lashe gasar.

Kungiyar Kwallon Kwando ta Najeriya, D'Tigers, ta lashe gasar kwallon kwando ta Afirka ta shekarar 2015 wadda aka kammala a Tunisia bayan ta doke Angola da ci 74-65.

Kungiyar ta kuma samu tikitin kai-tsaye daya tilo da aka ware wa Afirka a gasar Olympics ta 2016 a birnin Rio na Brazil.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya taya kunigyar murna, yana mai shan alwashin taimaka mata wajen samun nasara a wasanninta.

Wannan shi ne karon farko da Najeriya ta taba lashe gasar tun da aka fara ta.

Angola ce kasar da ke rike da kambun kwallon kwando na Afirka kafin Najeriya ta doke ta.