Odegbami zai tsaya takarar kujerar Fifa

Image caption Odegbami tsohon dan wasan Super Eagles ne

Tsohon dan wasan tawagar Nigeria, Segun Odegbami ya bayyana aniyarsa ta son zamowa shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya.

Odegbami mai shekaru 63, wanda ya lashe kofin nahiyar Afirka a matsayin dan wasa a 1980, shi ne na biyu dan Afirka da ya bayyana son zama shugaban hukumar, bayan Musa Bility na Liberia.

Ya kuma shaida wa BBC cewar "Ya kamata Afirka ta taka mahimmiyar rawa a fagen kwallon kafar duniya".

Duk dan takarar da yake da sha'awar maye gurbin Sepp Blatter, yana da wa'adin zuwa 26 ga watan Oktoba domin samun goyon bayan mambobin Fifa.

Za a yi zaben shugaban Fifan ne a ranar 26 ga watan Fabrairu, wanda Michel Platini da Chung Mong-joon suka bayyana aniyarsu ta son jagorantar hukumar.