West Brom ta fita daga ran Saido Berahino

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ran Berahino ya dugunzuma da West Brom ta hana shi barin kungiyar a bana

Saido Berahino ya ce ba zai sake buga wa West Brom tamaula ba karkashin jagorancin Jeremy Peace, bayan da kungiyar ta ki sallama wa Tottenham shi a ta yi biyu da ta yi.

Tun farko Tottenham ta taya Berahino sau biyu a baya, kuma an yi zawarcin dan wasan karo biyu a ranar da za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Ingila.

Berahino ya rubuta a shafinsa na Internet cewar "Ba zai iya bayyana abin da kungiyar ta yi masa ba, amma zai iya fada kai tsaye cewar ba zan sake buga tamaula karkashin jagorancin Jeremy Peace ba.

Tun a baya Shugaban West Brom, Jeremy Peace ya ce bai sauya batun da ya yi ranar 18 ga watan Agusta ba, inda ya ce ba su da niyyar sayar da Berahino a bana.

Tony Pulis bai saka Berahino a wasan Premier da West Brom ta yi guda biyu a baya ba, kuma kocin ya ce ya yi hakan ne domin dan kwallon ya samu natsuwa.